Kaza
Kaza | |
---|---|
Scientific classification | |
Class | Aves |
Order | Galliformes (mul) |
Dangi | Phasianidae (en) |
Genus | Gallus (en) |
subspecies (en) | Gallus gallus domesticus ,
|
General information | |
Tsatso | chicken breast (en) , chicken as food (en) da chicken egg (en) |
Kimanin bugun zuciya | 275 beats per minute (en) |
Wannan mukalar bata da Reference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da Reference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
. |
Kaza wata tsuntsuwa ce na daga cikin jinsin tsuntsaye wadanda ake ajiyewa a gida domin kiwo. Mutane nayin kiwon kaji ne domin amfana da naman su ko kuma kwansu ko kuma don a sayar domin kudi. Kaza tana yin kwanta dakanta kuma ta kyankyashe kayanta ba kamar wasu nau'in tsuntsaye ba, da basa iya kyankyashe kwansu. Namijin kaza shi ne ake kira da zakara mace kuma ana kiranta da kaza. Akwai kazar Hausa da kuma kazar Bature wadda inji yake kyankyashe su. Sannan akwai kazar Fulani.
irin wacce Fulani suke kiyo, girman kajin Fulani ya banbanta da sauran kaji, saboda yadda Fulani suke kiwon nasu. Har ila yau kaza dai nama ce mai farin jini wajen mutane saboda naman kaza ya banbanta da sauran namann tsinsaye. Naman kaza yana daya daga cikin naman da aka fi ci a duniya.
Ita kaza tanada baiwar kyankyashe kwayayenta, amma wasu halittun tsuntsaye irin su zabbi da talatalo har da Agwagwa takan kyankyashe kwansu idan an sanya mata. Har ila yau kaza tana kan gaba acikin tsuntsaye da aka fi siya a duniya, kuma da aka fi ci, saboda dadinta da kuma wasu sinadarai da yake tattare da ita.
Rabe-raben kaloli na kaji
[gyara sashe | gyara masomin]Akwai kala kala a cikin jinsin kaji, kamar baka da fara da ja, sai kuma masu hade da kaloli kamar mai ja da baki dama wani ratsi na fari ko shudi, ko kuma mai digo na fari da baki a dukkan jikinta. Akwai kuma nau'in kaza da ake kira nama wuya wanda zaka gansu babu gashi a wuyan su.
Kalli hotunan Kaji
[gyara sashe | gyara masomin]-
Kwayayen kaji